Gwamnatin Najeriya ta gargadi masu shirya bidiyoyi a kafar Sadarwa da su guji aibata Najeriya
Gwamnatin Tarayya ta yi kakkausan gargadi ga masu kirkirar bidiyoyi da ma’abota kafar Sadarwar zamani da su sassaita kalaman batancin da suke wallafawa a shafukansu na sada zumunta game da Najeriya.
Gwamnati ta dora musu alhakin da su ba da fifiko ga muradun al’umma ta hanyar bin ka’idoji, da Ɗa’a mafi girma yayin faɗin albarkacin bakinsu da isar da saƙonninsu.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ne ya yi wannan gargadin a ranar Juma’a a Abuja, a wani taron murnar makon kafafen yaɗa labarai na ƙasa na shekarar 2024.
Idan muna son Najeriya ta ci gaba, to bai kamata mu riƙa nuna munanan abubuwa a koyaushe ba.
Duk da yake yana da muhimmanci mu soki Gwamnati da sauran shuwagabanni domin aikin yada labarai ke nan, amma yana da matuƙar muhimmanci a wajen bayar da rahotonmu mu fifita mutuncin ƙasa.
“Ba za mu iya tsammanin Æ™asarmu za ta bunÆ™asa ba, kuma mutane su zo su saka hannun jari ba yayin da duk abin da muke wallafawa a kowane lokaci yana nuna aibu ga Najeriya.
“Akwai bayanai masu kyau da yawa da ke fitowa daga Najeriya, kuma ya zama wajibi mu kasance masu kishin kasa yayin da muke bayar da rahoto domin Najeriya ta kai ga inda take so, kamar yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake ta yin kira a kai,” in ji shi.
Ministan ya yi Allah-wadai da yaduwar labaran karya a shafukan sada zumunta, inda ya yi gargadin cewa, idan ba a dakile hakan ba, zai iya haifar da barazana ga haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban ƙasar.
Ya kuma yabawa hukumar UNESCO bisa jajircewar shirin duniya na daƙile yaduwar labaran ƙarya, musamman a Najeriya, ta hanyar kafa cibiyar wayar da kan jama’a ta ƙasa da ƙasa a ƙasar nan.
Daga Lukman Aliyu Iyatawa